BBC navigation

Wenger na sa ran komowar Jack Wilshere filin wasa

An sabunta: 21 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:07 GMT
jack wilshere ya buga kwallo

Jack Wilshere

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger ya sanar da cewa dan wasan Ingila mai buga wasa a tsakiyar fili, Jack Wilshere zai komo wasa cikin natsuwa bayan ya shafe watanni 14 yana jinya.

Wilshere ya samu rauni a didige a lokacin wasan sada zumunta a gabanin soma wasannin kakar wasa a watan Agusta na shekarar 2011, abin da ya sa bai yi wasanni ba a dukkan kakar wasanni ta 2011-2012.

Dan shekaru 20 da haifuwa ya dawo samun horo a fili, sai dai Wenger ya ce kulob din na bukatar taka tsantsan.

Wenger ya ce : " Jinyar da ya yi za ta sa ya samu karfin jiki. Yana da kyau kuma gwaji ne kan natsuwarsa ."

Wilshere bai yi wasannin Euro na 2012 ba,sakamakon fama ciwon da yayi a lokacinda yake murmurewar karayar da ya samu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.