BBC navigation

Kyaftin din Man U ba zai yi wasa ba na mako 8

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:35 GMT

Nemanja Vidic

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ba zai yi wasa ba har zuwa makonni takwas saboda aiki da akayi masa a gwiwarsa.

Nemanja Vidic bai buga wasan da Manchester United ta kara da Liverpool ba, saboda ya yi korafin yana jin ciwo a gwiwarsa ta dama.

Haka kuma gwaje-gwaje da akayi na nuni cewar matsalar zata kara kamari fiye da yadda akayi tsammani da farko, saboda haka dan wasan bayan na tsakiya an tilasta ayi masa tiyata.

Kochiyan Kulob din Sir Alex ferguson ya ce dan wasan an yi masa tiyata saboda haka ba zai buga wasa ba har tsawon mako takwas.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.