BBC navigation

Najeriya ta kira Mikel Obi wasa da Laberiya

An sabunta: 25 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:44 GMT

Mikel Obi

Najeriya ta kirawo gogaggen dan wasan nan na Chelsea Mikel Obi, don ya buga wasan da kasar za ta buga da Liberiya a gasar cancantar shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika.

Mikel ya fice daga tawagar a wasan Monrovia da akayi canjaras da ci biyu da biyu, amma an sake kiran sa don buga wasan na watan Octoba wanda za ayi a garin Calaba.

Mikel dai bai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasa ba, tun da Stephen Keshi ya zama kochiyan kungiyar.

Masu nazarin kwallon kafa a Najeriya na ganin kiran alamun nasara ne ga Najeriya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.