BBC navigation

Hukumar FA ta tuhumi kocin Wigan

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:59 GMT
robero martinez

Robero Martinez

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, ta tuhumi kocin kungiyar Wigan Roberto Martinez saboda kalaman da ya furta bayan da kungiyarsa ta sha kashi da ci 4-0 a hannun Manchester United.

Kocin ya zargi alkalin wasan ne da nuna goyon baya ga kungiyar Manchester United a gidanta Old Trafford a duk lokacin da take wasa a filin kuma ya na ganin kamata ya yi alkalin wasan ya kori danwasan United Danny Welbeck a lokacin wasan na ranar 15 ga watan Satumba.

Alkalin wasan a wannan karawa ya baiwa United bugun daga- kai- sai-maitsaron gida wadda Manchestern ba ta ci ba bayan da maitsaron gidan Wigan din Ali Al Habsi ya yiwa danwasan keta kamar yadda alkalin wasan ya yanke hukunci.

Tuhumar dai ta shafi dokar hukumar kwallon kafar ta Ingila ce mai lamba E3 wadda ta shafi Magana da wata kafar yada labarai kan abinda ka iya zubar da mutunci da kimar alkalan wasa ko kuma ma duk wani jami’I day a shafi wasa.

Kocin na wigan yana da wa’adin har zuwa karfe 4 na yamma ranar Alhamis ya kare kansa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.