BBC navigation

Hukumar FA ta sami John Terry da laifi

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:05 GMT
terry, ferdinand

Terry da Ferdinand

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila FA, ta dakatar da tsohon kyaftin din Ingila John Terry wasanni hudu bayan da ta same shi da laifin yin kalaman wariyar launin fata ga dan wasan Queens Park Rangers Anton Ferdinand.

Har ila yau Hukumar ta kuma ci tarar Terry fan dubu dari biyu da ashirin a bisa samunsa da wannan laifi wanda a watan Yulin da ya gabata wata kotu ta wanke shi daga wannan tuhuma.

Hukuncin dai ba zai tabbata ba har sai danwasan na Chelsea ya yanke shawarar abin da zai yi walau ya daukaka kara cikin kwanaki 14 ko kuma ya amince.

Yanzu dai ya nemi da a bashi bayanin bincike da matakin da Hukumar ta bi ta kai ga wannan hukunci dalla-dalla a rubuce kafin ya san ta yi.

Tun da farko dai lauyoyin John Terryn sun ce bas u ga dalilin da Hukumar kwallon ta Ingila zata binciki batun ba saboda kotu ta wanke shi amma hukumar ta ce nata binciken daban yake da na kotu.

A kan hakan ne kuma tsohon kyaftin din na Ingila ya sanar da ritayarsa daga bugawa Ingila wasa kwana daya kafin Hukumar ta FA ta fara zaman tuhumarsa.

Wani abin da aka zuba ido da kuma saurare a ji shi ne wana mataki kungiyarsa ta Chelsea zata dauka a kansa dangane da wannan hukunci kasancewar kungiyar bata lamuntar duk wani abu da ya danganci wariyar launin fata, za ta dakatar das hi ne ko zata ajiye shi ko kuma zata mara masa baya?

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.