BBC navigation

Podolski yana so Arsenal ta yi hangen nesa

An sabunta: 29 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:09 GMT

Lukas Podolski

Dan wasan gaba na Arsenal Lukas Podolski ya ce lokaci ya yi da kulob din zai manta da abin da ya faru a baya, watau ficewar da 'yan wasa kamar Robin van Persie da Alex Song suka yi daga cikinsa, sannan ya fara tunanin yadda zai ci gaba.

Podolski ya ce ya kamata kulob din ya fara yin nazarin yadda zai rika zura kwallaye a raga a wasannin da ke gabansa tun da akwai sababbin 'yan wasa irinsa, da Santi Cazorla da kuma Olivier Giroud.

Ya kara da cewa duk da yake ya so ganin Van Persie da Song sun ci gaba da zama a kulob din amma bai kamata ficewarsu ta kashe gwiwar Arsene Wenger ba.

Ya shaidawa jaridar Daily Mail cewa: " Zai fi kyau da a ce Robin Van Persie da Alex Song sun ci gaba da zama cikin kulob din, amma ko babu su yanzu akwai Cazorla da Giroud. Manyan 'yan wasa sun fice daga kulob din sai dai ba dace hakan ya sanyaya gwiwarmu ba."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.