BBC navigation

Ferguson ya koka da rashin karin lokaci

An sabunta: 30 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 18:23 GMT
alex ferguson

Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya koka tare da nuna bacin ransa a kan rashin bada karin lokaci a lokacin wasan kungiyarsa da Tottenham wanda aka ci United 3-2.

Kocin yana ganin ya kamata Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila ta karbe ikon kula da lokacin wasa daga hannun alkalan wasa, domin yana ganin idan da an kara lokaci kamar yadda ake yi a wasanni a karshe da Tottenham ba ta yi galaba a kan kungiyarsa ba.

Shekaru 23 ke nan rabon da Tottenham ta sami nasara a kan Manchester United a Old Trafford tun 1989.

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas mai shekaru 34 dan kasar Portugal ya ce sakamakon wasan na daga mafi kyawun sakamakon da ya samu a Ingila kuma yana alfahari da shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.