BBC navigation

Fernandes na goyon bayan Mark Hughes

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:03 GMT
Shugaban QPR, Tony Fernandes

Shugaban QPR, Tony Fernandes

Mai kungiyar QPR Tony Fernandes ya goyi bayan manajan kungiyar Mark Hughes duk kuwa da irin mummunan mafarin da kungiyar ta yi a gasar Premier.

Kungiyar dai ba ci nasarar ko da wasa guda ba a gasar, kuma ta kasance kuran-baya a jerin kungiyoyin da ke cikin gasar bayan kulab din Westham ya samu nasara da ci 2-0 a jiya Litinin.

Wani martanin da Tony Fernandes ya mayar ga wani magoyin bayan kungiyar a shafinsa na twitter ya ce "ku kwantar da hankalinku. Ba iya wasanni shida da aka kara ne karshen gasar ba. Na koyi darasi shugabanni da dama.

"Mark zai gano bakin-zaren. Ku duba tarihinsa. Da ba don yawan 'yan wasanmu ya ragu zuwa goma ba da mun ci wasan.

"Muna da gogaggen manaja, da sabon filin wasa da kuma manyan 'yan wasa.

"wadannan za su kara mana karfi. Bayan haka da ma hanyar nasara cike take da kalubale."

Manajan QPR Mark Hughes ya yi amanna cewa kulab din zai tabuka abin kirki nan gaba, duk kuwa da cewa kulab ya tsira da maki biyu daga cikin wasanni shida da ya yi, ga kuma sababbin 'yan wasa goma sha biyu da ya saya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.