BBC navigation

Steven Fletcher zai buga wa Scotland wasa

An sabunta: 2 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:17 GMT
Steven Fletcher

Steven Fletcher

Manajan kungiyar kwallon kafa na kasar Scotland, Craig Levein ya ce Steven Fletcher zai bugawa kasar wasa.

Dan wasan zai shiga cikin 'yan wasan kungiyar a taka-ledar da Scotland za ta yi na neman shiga gasar cikn kofin kwallon kafa na duniya.

Kungiyar kwallon kafar ta Scotland za ta kara ne da kasashen Wales da Belgium a cikin wannan watan.

Rabon da Fletcher ya buga wa Scotland wasa tun wani wasan sada zumuncin da kasar ta yi da Northern Ireland, a watan Fabrairun 2011, inda Fletcher bai samu zuwa ba.

Levein Craig ya ce shigar da Fletcher cikin 'yan wasan "Ci gaba ne a gare ni da kuma sauran'yan kungiyar idan aka shigar da shi (fletcher)

Shigar da Steven Fletcher cikin 'yan wasan kasar Scotland din dai ya kasance ba-zata, bisa la'akari da dangantakar da ta yi tsami tsakaninsa da manajan kungiyar ta Scotland.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.