BBC navigation

Robin van Persie ya ce zai kara himma

An sabunta: 3 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:39 GMT
Robin van Persie

Robin van Persie

Dan wasan gaban Manchester United, Robin Van Persie, ya ce zai kara himma wajen tallafa wa abokan wasansa don ci wa kulob dinsu kwallaye.

Ya yi wannan furucin ne bayan ya samu nasarar ci wa kulab din kwallaye biyu a wasan da suka yi da CFR Cluj ranar Talata.

Ya ce "Ina so na dinga taimakawa (ana cin kwallo). Sai daya na taimaka. Ina so na yi fiye da haka."

Wannan dai shi ne karo na farko da kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya hada Rooney da Van Persie suka yi wasa tare. Kuma su biyun ne suka hada-kai wajen ci wa Manchester kwallaye biyun da suka ba ta nasara a kan Cluj.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.