BBC navigation

Mutum 34 ke fatan zama Gwarzon Kwallon Afirka

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 11:03 GMT

A makwanni masu zuwa CAF za ta fitar da Gwarzon Kwallon Afirka

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka, wato CAF, ta sanar da jerin sunayen ’yan kwallo talatin da hudu, wadanda za ta zabi daya daga cikinsu ta ba shi kyautar Gwarzon Dan Kwallon Afirka na bana.

Daga cikin zaratan 'yan kwallon talatin da hudu akwai ’yan Najeriya su uku—John Mikel Obi, da Victor Moses, wadanda ke buga kwallo tare da Chelsea a Ingila, da kuma dan wasan kungiyar Montpelia a Faransa, John Utaka.

Daga Kamaru, Samuel Etoo, wanda a baya ya samu kyautar har sau hudu, na cikin masu neman samun kyautar ta bana, shi da Alex Song na Barcelona, da kuma Nicolas Nkoulou.

Matashin dan wasan Ghana, Andre Ayew, wanda ke bugawa kungiyar Marseille ta Faransa kwallo, da Emmanuel Agyemang-Badu, da kuma Kwadoh Asamoah, su ne ’yan Ghana uku da sunayensu suka fito a cikin jerin.

Gwarzon Dan Kwallon Afirka na bana, wato Yaya Toure na Manchester City, da Didier Drogba, da Arouna Kone, da Gervinho, da kuma Chieck Tiote na Newcastle, su ne ’yan Ivory Coast din da aka saka a cikin jerin.

A Disamba za a sanar da zakara

Demba Ba, da Pappis Cisse, da Papa Moussa Kounate—suna cikin ’yan Senegal hudu a jerin.

Sauran wadanda ke hararar wannan kyautar ta Gwarzon Dan Kwallon Afirka sun hada da Seydou Keita na Mali, da Adel Taarabt na Morrocco, da kuma Christopher Katongo na Zambia.

A makwanni masu zuwa ne hukumar CAF za ta yi tankade da rairaya, lokacin da za ta mayar da jerin zaratan ’yan kwallon ya koma mutane biyar kafin ta sanar da Gwarzon.

A bara dai dan kwallon Ivory Coast wanda ke taka leda a Manchester City, Yaya Toure, aka baiwa kyautar ta Gwarzon Dan Kwallon Afrika.

Ranar 20 ga watan Disamba ne za a sanar da dan kwallon da za a baiwa kauyatar ta bana a wani buki na GLO-CAF Awards da za a yi a birnin Accra na Ghana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.