BBC navigation

Ashley Cole ya nemi afuwar hukumar FA

An sabunta: 5 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:50 GMT
Ashley Cole

Ashley Cole

Mai tsaron baya na tawagar 'yan wasan kwallon kafar Ingila da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Ashley Cole, ya nemi afuwa saboda sukar Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Ingila, wato FA, da ya yi bayan an diga ayar tambaya a kan shaidar da ya bayar a shari'ar John Terry.

Wata hukuma mai zaman kanta ta hukumar FA ce dai ta yi tababar kalaman da Cole ya furta na goyon bayan Terry bayan ta samu Terry da laifin furta kalaman wariyar launin fata ga Anton Ferdinand yayin wani wasa tsakanin Chelsea da Queenspark Rangers a kakar wasanni ta bara.

A shafinsa na Twitter Cole, mai shekaru talatin da daya, ya rubuta wadansu kalamai marasa dadi a kan hukumar ta FA; daga bisani ya goge kalaman sannan ya wallafa sanarwar neman afuwa.

A sanarwar, Cole ya bayyana cewa: "Na kammala horo ke nan sai na ga abin da hukumar ta FA ta fada a kai na a akwatin talabijin.

"Abin da ya harzuka ni ke nan ya sa cikin fushi na rubuta abin da na rubuta. Amma dai ina neman gafara saboda abin da na rubuta a kan hukumar FA".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.