BBC navigation

Hukumar FA ta tuhumi Cole da aikata rashin da`a

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:53 GMT
ashley Cole

FA na tuhumar Ashley Cole

Hukumar kwallon kafa ta Birtaniya, wato FA ta tuhumi Ashley Cole da aikata rashin da'a sakamakon wani martani da ya mayar wa hukumar ta shafin twitter.

Cikin martanin da ya mayar game da hukuncin da hukumar FA ta yi a kan da shari'ar nuna wariyar launin fata da ta yi wa dan kwallon kafar nan John Terry, ranar Juma'ar da ta gabata, Ashley Cole cewa ya yi "hahahahaa, da kyau #fa, na yi karya ko? 'yan daba."

Hukumar kwallon kafar Birtaniyar ta bai wa Ashley Cole wa'adin nan da ranar Alhamis mai zuwa domin ya mai da martani.

Wata sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an tuhumi Ashley Cole da aikata rashin da'a ne saboda kalaman da ya yi a shafin twitter, wadanda hukumar ta ce ba su dace ba, wadanda kuma za su janyo zubewar martabar wasan kwallon kafa a idon al'uma.

Kalaman da Cole ya yi dai sun biyo bayan wani bincike da wani kwamitin FA ya gudanar ne, wanda kuma ya saurari bahasi daga Mr Cole dangane da zargin da aka yi wa John Terry na nuna wariyar launin fata ga Anton Ferdinand a wasan da kulab din Chelsea ya yi da QPR bara, bahasin da kwamitin ke tababa a kansa.

Tuni dai Ashley Cole din ya nemi afuwar hukumar FA dangane da kalaman da ya yi, yana cewa lamarin ya yi matukar daga masa da hankali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.