BBC navigation

Hukumar FIFA ta soke nasarar Da Sudan ta samu a kan Zambia

An sabunta: 8 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:53 GMT
hukumarfifa

tambarin hukumar kwallon kafa ta duniya

Hukumar kwallon kafa ta Duniya, wato FIFA ta soke nasarar da kasar Sudan ta samu a wasan da ta yi da kasar Zambia na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi badi, inda aka tashi biyu da nema.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda wani dan wasan da bai cancanci taka leda a gasar ba mai suna saif Ali ya yi wa kasar Sudan wasa.

Hukumar FIFA ta kara da cewa kwamitin ladabtarwarta ya yanke hukuncin cewa bai kamata Saiif Ali ya yi wasa a karawar da aka yi a Khartoum ba, saboda haka kasar sudan ta yi asarar nasarar da ta samu an mika wa kasar Zambia. Yanzu kasar Zambia ta koma tana da ci uku a wasan.

Kazalika Hukumar FIFA ta yi wa Sudan din tara dala dubu shida da dari hudu da talatin

Da wannan hukunci, yanzu kasar Zambia ce gaba-gaba a rukunin D da maki shida, inda kasar Sudan ta koma ta uku da maki daya. Kasar Ghana tana da maki uku, yayin da Lesotho ta tashi a tutar babu.

Kasar Zambia dai ta kai karar Saif Ali kasancewar ya yi wasa bayan an ba shi katin gargadi biyu a jere a wasu wasannin da kasar Sudan ta yi, ciki har da wanda kasar Zambia ta ci Sudan a zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a watan Fabrairu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.