BBC navigation

An bude katafariyar cibiyar kwallon kafa ta Ingila

An sabunta: 9 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:30 GMT
st georges

St Georges Complex

A yau ne Yarima William da matarsa Kate suka bude sabuwar katafariyar cibiyar Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila da aka gina a kan kudi fam miliyan 105 a Staffordshire.

Cibiyar da aka sanyawa suna St George Park complex mai fadin eka 330 ta kunshi filayen wasa 11 da naurar sauya yanayi ta yadda za iya juya yanayi yazo dai dai da yadda ake bukata da wuraren koyarda 'yan wasa da masu horadda 'yan wasa da sauran duk wasu abubuwan da ake bukata wajen bunkasa wasan kwallon kafa.

Cibiyar za ta kasance sansanin dun-dun-dun ga dukkanin kungiyoyin wasa na Ingila 24 daga kanana zuwa manya.

An dai gina cibiyar ne bayan da aka gudanar da bincike a wasu fitattun cibiyoyi makamantanta a kasashen duniya daban-daban kamar su Faransa da Spaniya da Qatar da Australia tsawon shekaru 37.

A game da wannan cibiya kyaftin din Ingila Steven Gerrad ya ce kasancewar suna da filin wasan da duk duniya ba kamarsa yanzu kuma sun sami cibiyar horadda wasan da ba bu irinta a duniya ba yanzu 'yan wasan Ingila ba za su sami wat mafaka ba ta kasa cimma burinsu.

Sai dai shi kuma kocin Ingila Roy Hodgson gargadi ya yi da cewa ba wai cibiyar horadda wasa ce abar dogara wajen samun nasara ba, cigaba ya dogara ne ga yadda aka yi amfani da cibiyar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.