BBC navigation

Yabon da Rooney ya yi min ba zai rude ni ba, inji Hart

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:45 GMT
joe hart

Joe Hart

Maitsaron gidan Manchester City Joe Hart ya ce ba zai bari yabo da kudar da Wayne Rooney ya yi masa kan bajintar da ya nuna a wasan da City ta yi kunnen doki 1-1 da Borussia Dortmund ba a makon da ya wuce ta rude shi.

Bayan wasan ne na Kofin Zakarun Turai Wayne Rooney ya jinjinawa golan na Manchester City da cewa a duk duniya ba kamarsa.

Sai dai Joe Hart wanda ya nuna godiyarsa ga Rooney a kan yabon yana mai cewa ''karramawa ce ta musamman ga wasu mutane su fadi abu mai kyau game da mutum amma a harkar tsaron gida a wasan kwallo reshe na iya juyewa da mujiya cikin kwanaki biyu kacal bayan ka zama tauraro''.

Hart dan shekara 25 ya yi kokari matuka wajen hana kungiyar Dortmund jefa kwallaye a ragar City in banda daya da ta sami nasara wadda kuma Mario Balotelli ya ramawa City din da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a dai dai minti na 90.

Hart wanda ya ke bayani ya yin da Ingila ke shirin karawa da San Marino a wasan neman shiga gasar cin Kofin Duniya a Wembley ranar Juma'a ya ce dole ne mutum ya yi kaffa-kaffa kada ya dauki girman kai ya dorawa kansa idan kuwa ba haka ba muddin ya aikata wani abu ba dai-dai ba zai ji kunya matuka.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.