BBC navigation

Majalisar Musulman Burtaniya ta soki Newcastle

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:33 GMT
Demba Ba na Newcastle

Duka wadannan 'yan wasan na Newcastle Musulmai ne Demba Ba, Papiss Cissé, Cheick Tioté and Hatem Ben Arfa

Majalisar Musulman Burtaniya ta yi Allah wadai da yarjejeniyar da Newcastle ta kulla da wani kamfanin bayar da bashi, inda ta nemi musulman 'yan wasan kulob din da kada su sanya tallan kamfanin.

Yarjejeniyar talla ta fan miliyan 24 tsakanin Newcastle da kamfanin Wonga.com na shan suka daga bangarori daban-daban a Burtaniya.

Babu shakka tsoma bakin da Majalisar Musulman Burtaniya ta yi zai kara rura wutar cece-kucen da ake yi, inda suka gargadi 'yan wasan kulob din musulmai cewa sanya jesin Newcastle da tallan Wonga.com ya sabawa dokokin shari'ar Musulunci.

Hudu daga cikin 'yan wasan Newcastle da suka buga wasansu da Manchester United ranar Lahadin da ta gabata, musulmai ne - Demba Ba, Papiss Cissé, Cheick Tioté da Hatem Ben Arfa.

'Bai kamata ba'

Wonga, wanda kwantiraginsa za ta fara da Newcastle badi, na cajar kudin ruwa mai yawan gaske a kan basukan da ya ke bayarwa na kwanaki talatin. Idan karanci fan 50 domin sayen jesin Newcastle, za ka biya fan 71.92 bayan wata guda - wanda zai ninka sau 4,212 a shekara daya.

Sakataren Majalisar musulmai ta Burtaniya Sheikh Ibrahim Mogra, ya shaida wa BBC cewa 'bai kamata 'yan wasan su sanya wannan riga mai dauke da tallan kamfanin Wonga ba.

"A zahiri take cewa addinin musulunci ya hana shiga harkar caca, ko riba, ko ganganci, a cewarsa. "Muna kallon wannan a matsayi daya da tallan giya wanda a zahiri take cewa musulunci ya haramta.

"Bamu yi magana da Newcastle ko musulman 'yan wasansu ba, kuma bamu da shirin yin haka. Mu dai kawai wa'azi ne aikinmu amma ba za mu tilastawa kowa bin doka ba, tunda mu ba gwamnati ba ce."

'Babu tilas sai dai shawara'

"Asali bai kamata su sa wannan rigarba, amma idan har abin zai shafi sana'arsu, kuma tunda ba doka ce gwamnati ta shinfida wa kowa dole sai yayi ba, to bai kamata a takura su ba, a cewar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano.

"Na farko ba su suka dau bashinba, ba kuma cewa suka yi lallai sai wani ya dauka ba, abune na ganin dama, ina ga bai kamata a takura su sai sun cire ba musamman idan zai shafi sana'arsr, ko aikinsu wacce kuma ta fi komai muhimmanci.

Dangane da batun cewa lamarin daidai yake da tallan giya kuwa, sai Sheikh Daurawa ya ce:

"Akwai banbanci tsakanin wannan da tallan giya, saboda asalin giya ko naman alade misali haramunne, amma wannan asalinsa halal ne sai dai haramun ka iya shiga ciki - wanda kuma mutum zai iya amfani da shi idan ya samu kansa cikin takura".

Kungiyar Newcastle na kokarin ganin ta kawar da damuwar da ake yi kan shirin nata, ta hanyar cewa za ta sauya sunan filin wasanta daga Sports Direct Arena zuwa sunan asali na St James' Park.

Shi ma kamfanin Wonga yayi alkawarin zuba jari a shirin horar da matasa, wanda zai samar da aiki ga yara 'yan kasa da shekaru 15 da 'yan 16.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.