BBC navigation

Maiyuwuwa Yobo ba zai bugawa Najeriya wasa ba

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:14 GMT
joseph yobo

Joseph Yobo

Maiyuwuwa kyaftin din 'yan wasan Najeriya Joseph Yobo ba zai buga wasan da kasar za ta yi ba ranar Asabar mai zuwa na neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika da Liberia.

Dan wasan ya ji rauni ne a guiwarsa lokacin da ya ke yiwa kungiyarsa Fenerbahche dake Turkiyya wasa.

Yobo ya yi wasa a karawar da kasashen biyu suka yi a watan da ya gabata a Liberia inda suka tashi 2-2.

Amma ko a wannan karawar an yi canjinsa ne da Efe Ambrose bayan hutun rabin lokaci.

Dama dai tun kafin yanzu danwasan bai sami damar buga wasannin neman shiga gasar cin Kofin Kasashen Afrika da Rwanda da kuma na neman zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2014 da Najeriya ta yi da Malawi da kuma Namibia a farkon shekaran nan.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.