BBC navigation

Armstrong gawurtaccen mai amfani da kwayoyi - Usada

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:46 GMT
Dan wasan tseren keke, Lance Armstrong

Dan wasan tseren keke, Lance Armstrong

Hukumar yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari a wasanni ta Amurka, Usada, ta bayyana zakaran dan wasan tseren keken nan Lance Armstrong a matsayin gawurtaccen mai amfani da kwayoyin kara kuzari.

Hukumar ta ce Armstrong ya yi cutar da ba a taba ganin irinta ba a fagen wasanni, wajen amfani da kwayoyin kara kuzari a kai-a-kai.

Tuni dai hukumar ta haramtawa dan wasan mai shekaru 41, tseren keke a fadin rayuwarsa tare da soke dukkan lambobin yabon da ya samu a baya guda bakwai, na gasar Tour de France.

A yanzu kuma Usada ta bada bayanin dalilan da yasa ta dauki wannan mataki, inda ta yi amfani da hujjojin da ta samu daga tsofaffin mambobin tawagar da yake ciki.

Armstrong dai ya sha musanta yin amfani da kwayoyin kara kuzari.

Sai dai dan wasan da ya fito daga jihar Texas bai kalubalanci zargin da ake masa ba.

Lauyan Armstrong, Sean Breen ya bayyana rahoton na Usada a matsayin 'Aikin shati fadi'

Martanin dai da ya fito daga shi kansa Armstrong din, kawai ya fito ne ta dandalin sa da zumunta na Twitter, inda ya rubuta cewa, " Me nake yi a ranar Laraba da daddare? Na fita shan iska da iyalina, ko a jikina abin da kawai nake tunani shi ne wannan" Inda ya yi nuni da shafin intanet dinsa na Livestrong.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.