BBC navigation

An cire Camara a matsayin ministan wasanni

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:21 GMT
titi camara

Titi Camara

Tsohon dan wasan Liverpool Titi Camara ya rasa mukaminsa na ministan wasannin Guinea sakamakon wasu sauye-sauye da gwamnatin kasar ta yi a majalisar ministocinta.

Dan wasan mai shekaru 39 wanda ya rike mukamin kyaftin da kuma kocin 'yan wasan kasar yana daga cikin ministocin da gwamnati ta sauya.

A shekarar 2010 ce aka nada shi a matsayin ministan, abin da ya sa ya zama tsohon dan wasa na farko da ya rike mukamin gwamnati a kasar.

A game da cire shi daga mukamin Camara ya ce ya na farin ciki da nasarar da ya samu a matsayin ministan na tsawon watanni 21 da ya yi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.