BBC navigation

An baiwa Rooney kyaftin din Ingila

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:33 GMT
wayne rooney

Wayne Rooney

An baiwa Wayne Rooney matsayin kyaftin din Ingila na wasan neman shiga gasar cin Kofin Duniya da kasar zata yi da San Marino gobe Juma'a a filin wembley.

An baiwa dan wasan mai shekaru 26 mukamin ne sabo da rashin Steven Gerrad wanda aka dakatar da kuma Frank Lampard wanda ya ji rauni.

Rooney wanda sau 76 ya na bugawa Ingila wasa ya ce ''wannan wani abu ne da ya ke matukar alfahari da shi''.

Ya kara da cewa ''babban kalubale ne gare ni kuma ina matukar farin ciki, tare da fatan zamu sami nasara a ranar''.

A kan shirye-shiryen da kocin na Ingila Roy Hodgson ya ke yi game da wasan na gobe ya ki ya bayyana 'yan wasansa 11 da zai sa, ko da ike dai bai nuna wata damuwa ba a game da wasan da San Marino wadanda wasansu daya kawai su ka ci kuma su ka yi canjaras a biyar daga cikin wasanni 114, kuma a ka jefa kwallaye 473 a ragarsu.

Roy Hodgson ya ce shi ya san ko su wa ya sa a wasan ya san za su yi nasara.

Rooney ya taba rike mukamin na kyaftin lokacin da suka yi wasa da Brazil da ta ci su 1-0 a watan Nuwamba na 2009 sa'ilin da aka jiwa John Terry wanda yanzu ya yi ritaya rauni.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.