BBC navigation

Ya kamata Terry ya fuskanci haramci kamar Suarez - Triesman

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:56 GMT
Tsohon shugaban hukumar kwallo na Ingila, Lord Triesman

Tsohon shugaban hukumar kwallo na Ingila, Lord Triesman

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na Ingila, Lord Triesman ya ce ya kasa fahimtar dalilin da yasa aka sassauta wa John Terry haramcin buga wasa, kasa da na Luis Suarez na Liverpool.

Ita dai hukumar kwallon kafar ta ce, ta yi wa Kyaftin din Chelsea sassauci ne saboda ya yi amfani da kalaman nuna wariyar launin fata sau daya.

Sai dai Lord Triesman ya ce shi baiga banbancin ba.

"Watakila idan ka dubi bayanan, sun yi tsammani akwai banbanci, amma ni ban gan shi ba." Inji Triesman.

An haramtawa Terry buga wasanni hudu tare da cinsa tarar fam dubu 220 saboda muzanta Anton Ferdinand.

Yayin da Suarez kuma aka haramta masa wasa takwas saboda irin wannan laifin da ya aikata a kan Patrice Evra a bara.

Sai dai an gano cewa Suarez ya yi ta maimaita kalaman cin mutuncin a kan dan wasan bayan na Manchester United.

Triesman ya bayyana cewa "Na yi magana da 'yan wasa bakake da dama, wadanda na sani a lokacin ina jan ragamar hukumar kwallon kafa ta Ingila, kuma mafi yawa daga cikinsu sun ce mini 'kace za a samu cigaba, mu ba mu ga cigaban da aka samu ba."

"Ina ganin suna cikin matukar damuwa, kuma suna da hujjar hakan, domin a ganina babu batun ba sani ba sabo a harkar. Kuma matakan ladaftarwar da ake dauka ba na bai daya ba ne. " Inji Triesman.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.