BBC navigation

Toure ya lashi takobin cigaba da fafatawa a City

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:00 GMT
kolo toure

Kolo Toure

Dan wasan Manchester City Kolo Toure ya ce zai yi duk abin da zai iya domin ya dawo cikin 'yan wasan da ke kan gaba a kungiyar duk da cewa yanzu akwai mutane uku a gabansa.

Kocin kungiyar Roberto Mancini ya fi fifita Joleon Lescott da Vincent Kompany da kuma sabon dan wasan klub din Matija Nastasic a kan tsohon kyaftin din na City.

Amma duk da haka Toure dan shekara 31 ya ce yana son cigaba da zama a kungiyar ya yi gwagwarmayar komawa cikin jerin zaratan 'yan wasanta.

Dan wasan ya ce ''abu ne mai wuyar gaske, ina daga cikin muhimman 'yan wasan kungiyar, na yi komai amma wannan bai sa kocin ya sauya ra'ayinsa ba.''

Toure ya ce sauran 'yan wasan kungiyar da dan uwansa Yaya Toure sun san yana iyakar kokarinsa amma kungiyar ta na yi masa kora da hali yanzu, a don haka ya ce shi baya fushi da kocin, domin idan wani baya bukatarsa akwai wata kungiyar da ta ke son sa.

Game da yawan shekarunsa kuwa ya ce yana daukar Ryan Giggs mai shekaru 38 da Paul scholes dan shekara 37 a matsayin ababan koyi saboda har yanzu suna buga wasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.