BBC navigation

Messi ya yabawa magoya bayansa na Argentina

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:48 GMT

Messi a lokacin da ya zura kwallo a ragar Uruguay

Lionel Messi ya bayyana farin ciki saboda goyon bayan da magoya bayansa 'yan kasar Argentina suka nuna masa a lokacin da suka buga wasa na gasar neman cancantar shiga gasar kwallon duniya, inda suka ci Uruguay uku babu ko daya.

Fitaccen dan wasan Barcelona ya yi kokari sosai wajen ganin ya bugawa kasarsa wasa kamar yadda yake bugawa kulob dinsa amma hakan ya gagara, lamarin da ya sanya magoya bayansa 'yan Argentina ba sa jin dadi.

Sai dai dan wasan mai shekaru 25 ya samu damar cin kwallaye biyu a wasan da suka buga da Uruguay, wacce ita ce ta lashe gasar cin kofin kasashen kudancin Amurka a 2011, kuma hakan ya sanya kasarsa ta samu maki uku.

A cewarsa, yana matukar jin dadin bugawa kasarsa wasa.

Messi ya shaidawa manema labarai cewa:" Ina farin ciki a duk lokacin da na bugawa Argentina wasa.Yanzu da yake muna samun nasara, abubuwa na kara yin sauki kuma ina jin dadi. Ina farin cikin yadda magoya baya na 'yan Argentina ke nuna min kauna sosai. Sun nuna min kauna a River Plate, da Cordoba, da kuma Mendoza. Ina farin ciki magoya baya na na Argentina suna nuna min kauna kamar yadda magoya baya na a Barcelona ke nuna min."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.