BBC navigation

An kwantar da Peter Rufa'i a asibiti

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:30 GMT
yan wasan najerya

yan wasan Najeriya

An kwantar da tsohon mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Peter Rufa'i bayan da ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa dake Lagos ranar Litinin da daddare.

Peter Rufa'i mai shekaru 49 wanda ya bugawa Najeriya a gasar cin Kofin Duniya ta 1994 da 1998 ya suma ne bayan da ya fadin da hakan ya sa aka garzaya da shi asibiti.

Wani dan uwansa Bruce ya ce lamarin ya firgita su ganin cewa kafin hakan ta faru yana cikin koshin lafiya amma kwatsam sai ya fadi yana numfashi dai-dai.

Sai dai ya ce bayan sa'oi da dama da dan uwannasa ya yi a asibitin yanzu ya farfado yana samun sauki harma ya na gane mutane.

Amma ya ce likitocin ba su gano wata matsala tare da Peter din ba amma da alamu lamarin ba zai rasa nasaba da kaduwa da jimamin rashin mahaifiyarsu ba wadda ta rasu a makon da ya wuce ta na da shekaru 78.

Peter Rufa'i wanda ake masa lakabi da Dodo Mayana na daya daga cikin gwanayen masu tsaron gida da aka taba samu a nahiyar Afrika ya yi sana'ar wasan kwallon kafa a kasashen Benin da Belgium da Holland da Spain da kuma Portugal.

Tun lokacin da ya dena buga wasa ya yi kwamitin Olympic na Najeriya kuma yana gudanar da wata makarantar koyawa matasa kwallon kafa a Lagos.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.