BBC navigation

An garzaya da Peter Rufai zuwa asibiti

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:07 GMT

Tsohon dan wasan kwallon kafa na kasa a Najeriya Peter Rufa'i ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa dake Lagos.

Peter Rufa'i dan shekara 48 kamar yadda dan uwansa na jinni Mr. Bruce ya shaidawa BBC cewa a yanzu ana ci gaba da kula da lafiyarsa a asibitin Toki dake a Surulere.

Kawo yanzu dai likitoci basu yiwa manema labarai karin haske game da koshin lafiyarsa ba.

Sai dai dan uwansa yace ya na cikin koshin lafiya ya fara wartsakewa, kuma likitoci sun tabbatar masu cewa basu ga wata cuta a jikinsa bayan binciken da suka gudanar. Wadda ta dabaibaye shi , har ya yanke jiki ya fadi.

Bincike da BBC ta gudanar na nuni da cewa tun bayan mutuwar mahaifiyarsa Christiana ‘yar shekara 78 ,wadda bai samu sa-ta a ido ba , har ta bar duniya- na cikin abinda ake kyautata zato ya taba shi.

Wani amininsa ya shaidawa BBC cewa tun lokaci daya rasa mahaifiyarsa makon daya gabata, ya fita daga hayyacinsa.

Peter Rufa’i dai ya jima yana jan zarensa a matsayin babban mai tsaron gida a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa Green Eagles a Naijeriya.

Peter Rufa’i dai yana cikin masu tsaron gida 10 da suka shahara da aka taba yi a nahiyar Africa.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.