BBC navigation

Rooney na da sauran rawar da zai taka-Neville

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:59 GMT

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Gary Neville ya ce har yanzu Wayne Rooney na da sauran rawar da zai taka a matsayinsa na dan wasan kwallon kafa.

Ranar juma'a mai zuwa ne za a yi bikin cika shekaru goma da kwallon da Rooney ya zira a cikin ragar Arsenal yana mai shekaru goma sha shida, abun da yasa ya kasance matashi na farko mai kankanci shekaru da zira kwallo a gasar frimiya a wancan lokacin.

" A shekaru ashirin da shida, zaka rika tunanin ya kamata ka sake aiwatar da wani abun a zo a gani." Neville ya shaidawa BBC radio 5

Tsohon dan wasan baya na Ingila ya bayana Paul Scholes da Ryan Giggs a matsayin yan wasan da Rooney zai koyi darasi daga wurinsu .

"Ryan Giggs ya fara a matsayin dan wasan gefen hagu zuwa dan wasan dake wasa a kusan koina."

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.