BBC navigation

Harry Redknapp ya gargadi Croatia

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:20 GMT
Wales

Harry Redknapp

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Redknapp ya gargadi Croatia game da dan wasan kungiyar kwallon kafa na yankin Wales, Gareth Bale saboda matsayinsu daya da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

Yan wasan kwallon kafa Wales zasu ziyarci Croatia ranar talata a wasan neman cacantar shiga cikin gasar kofin duniya ta FIFA.

Bale ya taka rawar gani a nasarar farko da kungiyar kwallon kafa ta Wales ta yi a shekarar da muke ciki bayan ta lalasa Scotland da ci biyu mai ban haushi.

" Dan wasa ne mai kayartarwa, mai baiwa dake buga wasa irinsu Ronaldo da Messi ." Redknapp yace.

Dan wasan gefe na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da kwantaraginsa zai zo karshe a shekarar 2015, ya zuba kwallaye uku a raga a wasannin da kungiyar kwallon kafa ta Wales tayi a shekarar da muke ciki kuma kwallayen da dan wasan mai shekaru ashirin da uku ya zura a cikin ragar Scotland ya ba Chris Coleman damar samun nasarasa ta farko a matsayin kocin Wales.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.