BBC navigation

Serbia ta musanta zargin nunawa yan Ingila bambancin launin fata

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:19 GMT
ingila da serbia

Ingila da Serbia

Hukumar Kwallon Kafa ta Serbia ta musanta cewa an nunawa 'yan wasan Ingila 'yan kasa da shekara 21 wariyar launin fata a lokacin wasansu na Euro 2013 jiya Talata.

Kuma jami'an Hukumar sun dora wa dan wasan Ingila Danny Rose laifin tada hatsaniyar da a ka samu a karshen wasan saboda abin da suka kira rashin da'a da abin da bai dace ba da wasa.

Tun da farko dai Rose mai shekara 22 da bakar fata ne ya bukaci da a haramtawa Serbia shiga wasanni yana zargin cewa an ci mutuncinsa ta hanyar nuna masa wariyar launin fata a lokacin wasan.

Ingila ce dai ta yi nasara a wasan lokacin da Connor Wickam ya ci mata kwallonta daya tilo a dai-dai minti na 90 wanda hakan ya baiwa Ingila damar zuwa gasar cin Kofin Turai na 2013 na 'yan kasa da shekaru 21.

Daga jefa wannan kwallo da Ingilan ta yi ne sai hatsaniya ta barke a filin tsakanin 'yan wasa har ma da jami'ansu 'yan kallo kuma suka rinka jifa cikin filin, har kuma alkalin wasa ya kori dan wasan Ingilan Danny Rose saboda buga kwallon da ya yi cikin 'yan kallo da gan-gan.

Akan lamarin frai ministan Burtaniya David Cameron ya bukaci Hukumar Kwallon Kafa ta Turai UEFA, da ta rinka yin hukunci maitsauri a kan laifukan nuna wariyar launin fata, ya yin da shi kuma ministan wasanni Hugh Robertson ya aikawa shugaban Hukumar Kwallon ta Turai Michel Platini takardar korafi da zargin tsokana da nuna bambancin launin fata lokacin wasan.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.