BBC navigation

Hukumar FA ta ci tarar Ashley Cole fam 90,000

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:14 GMT
ashley cole

Ashley Cole

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, ta ci tarar dan wasan Chelsea Ashley Cole fam 90,000 a kan laifin yin kalaman batanci ga Hukumar a shafinsa na intanet na Twitter game da hukuncin da ta yiwa John Terry na nuna wariyar launin fata.

Dan wasan bayan na Chelsea da kuma Ingila mai shekara 31 ko da ike a lokacin da ya rubuta kalaman batancin ya yi sauri ya goge su tare dabada hakuri amma dai ya amince da tuhumar da Hukumar ta FA, ta yi masa na batancin da ake ganin ya shafi mutuncinta da kuma kimar wasan kwallon kafa a Ingila.

Cole ya ketare siradin haramta masa buga wasa saboda ya nemi gafara da daga shugaban Hukumar kwallon ta Ingila David Bernstein, abinda Bernstein ya ce ya nuna nadama sosai.

Bayan hukuncin tarar Hukumar ta kuma gargadi Ashley Cole wanda ya roke ta da kada ta gurfanar da shi a gabanta a kan kada ya sake aikata wani abu makamancin wanda ya yi a nan gaba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.