BBC navigation

An yabawa Rose kan nuna juriyar wariyar launin fata

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:30 GMT
danny rose

Danny Rose

Mahaifin Danny Rose dan wasan kwallon kafa na Ingila na kungiyar 'yan kasa da shekara 21 ya yabawa dan nasa saboda kin maida martani da ya yi a kan takalar 'yan wasan Ingila bakaken fata da magoya bayan 'yan wasan Serbia su ka yi na yin waken wariyar launin fata lokacin wasansu da Serbia.

Mahaifin dan wasan, Nigel, ya ce Rose ya cancanci yabo saboda wannan juriya da ya nuna shi da takwarorinsa da dukkanninsu ba bu wanda ya maida martani a kan cin mutuncin da aka yi musu.

A kan haka ya ce sun zama ababan alfahari ga kungiyarsu da kuma iyayensu.

Mahaifin nasa ya ce a zahiri ta ke magoya bayan 'yan wasan na Serbia sun rinka kukan biri don muzanta 'yan wasan na Ingila bakakn fata.

Hatsaniya ta barke ne a wasan bayan da dan wasan ingila Connor Wickham ya je kwallo a ragar Serbia a na minti na 90 da hakan ya bata nasara a kan serbia da kwallaye 2-0 hadi da kwallon karawar farko,wanda ya sa Ingila ta sami wucewa zuwa gasar Euro 2013.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.