BBC navigation

Jami'in Hukumar Kwallon Senegal ya yi Murabus

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:52 GMT
wasan senegan da ivory coast

wasan Senegan da Ivory coast

Mataimakin Shugaban hukumar kwallon Kafa ta Senegal ya ajiye aikinsa sakamakon rikicin da 'yan kallo su ka tayar a lokacin wasan kasar da Ivory Coast ranar Asabar da ya tilasta dakatar da wasan.

Louis Lamotte wanda shi ne jami'in tsara wasa na karawar ta Senegal da Ivory Coast ta neman shiga gasar cin Kofin kasashen Afrika a ranar wadda aka tsaida wasan ana minti na 74 bayan Ivory Coast ta ci kwallonta ta biyu, ya ce saboda matsayinsa na wasan wajibi ne ya dauki alhakin abin da ya faru a wannan rana ta Asabar.

Ya ce a kan haka ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa na mataimakin shugaban hukumar kwallon ta Senegal.

'Yan kallo magoya bayan Senegal sun tada rikici ne bayan da Didier Drogba ya ci wa Senegal kwallo ta biyu inda suka rinka jifa cikin fili da cinna wuta a filin wasan abin da ya sa alkalin wasa ya dakatar da wasan tsawon minti 40 daga bisani ma ya tashi wasan baki daya.

Akan rikicin Hukumar Kwallon kafa ta Afrika, CAF, ta dakatar da Senegal daga gasar kuma ta baiwa Ivory Coast nasara ta re da damar tsallakewa zuwa gasar cin Kofin Afrikan da za ayi a Afrika ta Kudu a watan Janairu.

Ana ganin akwai kuma yuwuwar hukumar ta CAF, ta kara hukunta Senegal din a kan amfani da filin wasan kasar na Dakar saboda rikicin kamar yadda ta yiwa Togo inda ta harmta mata amfani da wasa tsawon wata shida a filin wasan kasar saboda irin wannan laifi a 2007

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.