BBC navigation

John Terry ya ce ba zai daukaka kara ba

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:34 GMT
John Terry

John Terry

John Terry ya nemi afuwa bayan da ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba dangane da haramta masa buga wasanni hudu saboda samunsa da laifin furta kalaman wariyar launin fata ga dan wasan Queens Park Rangers (QPR) Anton Ferdinand.

Kyaftin na Chelsea dai ba zai buga wasannin kungiyar na gaba har guda hudu wadanda za ta buga a gida.

Wani kwamitin Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, ne ya same shi da laifin furta kalaman na wariyar launin fata yayin wani wasa tsakanin Chelsea da QPR ranar 23 ga watan Oktoban 2011.

A cewar Terry, "Ina so in yi amfani da wannan dama in baiwa kowa hakuri saboda irin lafuzzan da na yi amfani da su yayin wasan".

Dan wasan mai shekaru talatin da daya da haihuwa ya kuma kara da cewa: "Ko da yake hukuncin hukumar ta FA bai min dadi ba, na amince cewa kalaman da na yi amfani da su, ko ma mecece sigarsu, ba su dace a yi amfani da su a filin wasa ba".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.