BBC navigation

Al Ahly ta fitar da Sunshine Stars

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:41 GMT
yan wasan ahly

'Yan wasan Al Ahly

Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly ta Masar ta yi nasara a kan takwararta ta Sunshine Stars ta Najeriya da ci 1-0 a wasan kusa da na karshe na cin Kofin Zakarun Afrika.

Da wannan nasara Al Ahly ta sami galaba a kan Sunshine Stars din da ci 4-3, kasancewar a karawarsu ta farko a Najeriya sun tashi da ci 3-3.

A dai-dai minti na 28 ne dan wasan Al Ahly Gedo ya ci kwallon.

Yanzu za a yi wasan karshe tsakanin Al Ahly da Esperance na Tunisia karawa biyu a watan Nuwamba .

Kungiyar ta Al Ahly sau shida ta na daukar Kofin na Zakarun Afrika, ita kuwa kungiyar Sunshine wannan shi ne karon farko da ta sami shiga gasar.

An yi karawar ne tsakin kungiyoyin biyu a filin wasa na sojoji dake Alkahira ba tare da 'yan kallo ba saboda rikicin da aka yi da ya yi sanadiyyar hallaka 'yan kallo saba'in afilin wasa na Port Said a watan Fabrairu.

Rahotanni sun ce an jinkirta wasan da kamar mintina 30 saboda 'yan wasan Sunshine ba su zo filin wasan da wuri ba saboda wasu masu zanga-zanga sun taru a kofar otaldinsu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.