BBC navigation

Bolton na neman kociyan Crystal Palace

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:32 GMT
dougie freedman

Dougie Freedman

Kungiyar Bolton wadda ba ta da kociya ta nemi izinin takwararta ta Crystal Palace ta tattauna da kocinta Dougie Freedman ko yana da sha'awar komowa klub din.

A watan Janairu na 2011 Freedman ya zama kocin Palace inda ya maye gurbin George Burley.

A kakar wasanni da ta gabata ya kai Palace matakin wasan kusa da na karshe na cin kofin lig.

A ranar Asabar Bolton su ka sami nasara a kan Brstol da ci 3-2 a wasansu na farko tun bayan korar kocinsu Owen Coyle.

Kocin kungiyar matasan 'yan wasan Bolton Jimmy Phillips shi ne ke rikon mukamin Kocin a wucingadi kafin a nada wani sabo.

Wannan shi ne karon farko da Freedman mai shekaru 38 ya ke aiki a matsayin kociya bayan ya yi ritaya a matsayin dan wasa da ya bugawa kungiyoyin Barnet da Palace da Wolves da Nottingham Forest da Leeds da kuma Southend.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.