BBC navigation

John Terry zai daura kambun dantse na yaki da wariyar launin fata

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:15 GMT
shugaban uefa michel platni

Shugaban Uefa Michel Platini

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Turai, wato UEFA, za ta bukaci John Terry ya daura kambun yaki da wariyar launin fata a wasan Chelsea da Shakhtar Donetsk a Gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

UEFA, wadda ita ce hukumar da ke kula da Gasar, ta ce ''Kyaftin-kyaftin din kungiyoyi za su daura kambun dantse na yaki da wariyar launin fata''.

Yunkurin wani mataki ne da kungiyar yaki da wariyar launin fata a Turai ta dauka a wannan makon.

Kwanakin baya Terry ya amince da hukuncin da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Ingila ta yanke na dakatar da shi daga wasanni hudu, saboda samunsa da laifin nuna wariyar launin fata, da cin zarafin dan wasan QPR Anton Ferdinand.

Masu yekuwar Kick It Out ta yaki da wariyar launin fata a filayen wasa sun fuskanci matsala a lokacin da suka shirya makon kin wariyar launin fata, inda 'yan wasa kamar su Rio Ferdinand, Jason Robert da wadansu 'yan wasa talatin daga kungiyoyi takwas suka ki sanya rigar da kungiyar yaki da wariyar launin fata ta umarci a sanya.

Ranar 29 ga watan Oktoba lokacin da aka ware don yekuwar ta Kick It Out mai yaki da wariyar launin fata zai zo karshe.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.