BBC navigation

Dakarun Afrika a Somalia za su bar filin wasan Mogadishu

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:53 GMT

Dakarun Kungiyar Afrika

Dakarun Kungiyar Afrika a Somaliya na fatan janyewa daga sansanin ta a Filin wasa na kasar dake Mogadishu a lokacin da za a buga wasannin kwallon kafa a watan Disamban bana.

A farkon wannan makon ne dai Kungiyar kwallon kafa ta Somalia ta ce tana muradin filin wasan don yin wasanni.

Filin wasan mogadishu 'yan tawaye ne dai suka mamaye shi lokacin da aka fara yakin basasa a alif dari tara da casa'in da daya inda ya zama matattarar gungun samari dauke da bindigogi.

Kakakin Rundunar sojin Kungiyar Africa Col Ali Hamud ya shaidawa BBC cewa bukatar da Kungiyar kwallon kafar ta nema ba sabon abu bane.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.