BBC navigation

Freedman zai iya zama kociyan Bolton

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:59 GMT

Dougie Freedman

Ana saran Dougie Freedman zai zama kociyan Kungiyar kwallon kafa ta Bolton Wanderers nan da karshen wannan makon.

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta bawa Bolton damar magana da kochiyan mai shekaru talatin da takwas.

Sai dai babu tabbas ko Freedman din zai jagoranci Kungiyar Palace a wasan da za su kara da Kungiyar kwallon kafa ta Barsley ranar Talata.

Kulab din Bolton dai ba shi da kociya tun lokacin da ya kori kociyansa Owel Coyle ranar tara ga watan Oktoba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.