BBC navigation

Watakil Lampard ba zai buga wasan Chelsea da Man U ba

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:36 GMT

Dan wasa frank lampard

Ana sa ran Frank Lanpard zai samu bayani a kan ko yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya buga wasan Chelsea da Manchester United ranar Lahadi.

Minti goma sha takwas kadai dan wasan mai shekaru talatin da hudu ya yi a filin yayin wasan da kungiyar sa ta sha kashi a hannun Shakhtar Donetsk da ci biyu da daya a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ranar Talata bayan da ya yi rauni a sha-rabarsa.

Za a duba lafiyar dan wasan domin tabbatar da ko zai iya buga wasan da United a Stamford Brige.

''Tsohon ciwo ne ya taso masa'', in ji kocin kungiyar ta Chelsea, Roberto Di Matteo.

An dai taba cire sunan Lampard a jerin wadanda za su buga wasan Ingila da San Marino da kuma wasan Ingila da Poland na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya a farkon watan nan, saboda raunin da ya yi a sha-rabar tasa.

Di Matteo ya kara da cewa: "Ya yi atisaye da mu lami lafiya, kuma babu wata alama ta matsala kafin wasan; ya na da cikakkiyar lafiyar da zai buga wasa".

Kungiyar Chelsea ce dai ke saman teburi; tana gaba da Manchester United da maki hudu, bayan da ta yi nasara a wasanni bakwai cikin takwas din da ta buga.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.