BBC navigation

Mancini ya kare dabarun wasansa

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:40 GMT
Roberto Mancini

Kociyan kulab din Mancheter City, Roberto Macini

Kociyan kulab kwallon kafa na manchester City Roberto Mancini ya kare salon wasansa na amfani da masu tsaron tsakiya uku maimakon hudu baya-hudu tsakiya- biyu-gaba bayan Micah Richard ya nuna damuwa game da hakan.

Richard ya yi ikirarin cewa salon ne ya janyo musu kaye a karawar da suka yi da kulab din Ajax a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Amma Mancini ya ce kwararren dan wasa ba ruwansa da nau'in salo, kuma idan bai fahinci wannan ba to ba zai iya buga wa babban kulab kwallo ba.

Mancini ya ba da umurnin sauya salon wasa ga 'yan kulab dinsa ne lokacin da City ke gaba da ci daya da nema.

Sai dai sauya salon ke da wuya aka ci City kwallaye uku.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.