BBC navigation

Za a yi cincirundo a filin wasa a Afrika ta kudu-Roelf

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:05 GMT
Yana jawabi lokacin canken rukuni-rukuni

Jacob Zuma shugaban Afrika ta kudu

Manajan filin wasa na Mbombela a Nelspruit, Roelf Kotze, yana da kwarin gwiwar samun masu kallon wasannin gasar cin kofin Nahiyar Afrika da yawan gaske.

Filin wasan dai za a yi wasanni takwas har da wasannin zagaye na biyu da kuma na kusa da karshe.

Wasan da za a yi na farko na bude filin wasannin Mbombela shine karambattar da za a yi tsakanin masu rike da kambun gasar; Zambia da kuma Najeriya wanda za a yi ranar ashirin da biyar ga watan Janairun shekara mai zuwa.

Roelf yake cewa, " muna da kwarin gwiwar cewa za mu samu cincirundon 'yan kallo".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.