BBC navigation

Manchester City ta nada sabon Darakta

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:22 GMT

Kociyan Manchester City, Roberto Mancini

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta nada tsohon Daraktan Kungiyar kwallon kafa na Barcelona, Txiki Begiristain a matsayin daraktansu.

Daraktan mai shekaru arba'in da takwas zai duba harkokin daukar 'yan wasa; matsayin da Brian Marwood ya rike.

Tsohon dan gaban Arsenal Marwood an matsar da shi wani matakin a matsayin Manajan Daraktan kulab din.

Daukar Txiki Begiristain dai na nuni da cewa wani fitacce ne wanda ake girmamawa a harkar kwallon kafa a yankin gabashin Ingila.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.