BBC navigation

Alkalan wasa ne Makomar koken Chelsea

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:28 GMT
Roberto Di Matteo

Kocin Kulab din Chelsea

Wani tsohon alkalin wasan kwallon kafa, Graham Poll ya ce makomar koken da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi a kan wanda ya alkalanci wasan da ta yi da Manchester United ranar Lahadi, Mark Clattenburg ta dogara ne a kan shaidar da masu taimaka wa alkalin wasa za su bayar.

Kungiyar Chelsea ta yi zargin cewa alkalin wasan ya yi wa 'yan wasanta biyu kausasan kalamai ma su nuna wariyar launin fata.

Cikin wadanda ake zargin an yi wa munanan kalaman har da John Mikel Obi.

Tuni dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a koka a hukumance da halayyar alkalin wasa Mark Clattenburg bayan ta zarge shi da furta kalaman da ba su dace ba ga biyu daga cikin 'yan wasanta yayin wasan da ta sha kashi a hannun Manchester United da ci uku da biyu.

Tun bayan kammala wasan da kungiyar Chelsea ta yi da Manchester United Kociyan Chelsea Roberto Di Matteo ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda aka alkalanci wasan.

Ya ce "alkalin wasan ya yi wasu hukunce-hukunce biyu da ke cike da kura-kurai, wadanda kuma suka yi tasiri a kan sakamakon wasan, ciki har da jan katin kora daga fagen wasa da aka bai wa Fernando Torres.

"Ba mu ji dadi ba ko kadan. Kuma abin kunya ne a ce an tabka irin wadannan kura-kuran."

Ita ma Hukumar kwallon kafa ta Ingila a nata bangaren ta fara bincike a kan wannan zargin da kungiyar kwallo ta Chelsea ta yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.