BBC navigation

Chelsea ta koka da halayyar alkalin wasa

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:18 GMT
Mark Clattenburg da John Mikel Obi

Mark Clattenburg da John Mikel Obi

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta koka a hukumance da halayyar alkalin wasa Mark Clattenburg bayan ta zarge shi da furta kalaman da ba su dace ba ga biyu daga cikin 'yan wasanta yayin wasan da ta sha kashi a hannun Manchester United da ci uku da biyu.

An shaidawa BBC cewa wani bangare na zargin shi ne cewa Clattenburg ya yi amfani da kalaman da ke nuna wariyar launin fata, kuma al'amarin ya shafi John Mikel Obi.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta Chelsea ya ce: "Mun mika kokenmu a hukmance ga wakilin Gasar Premier a filin wasan; shi kuma zai mika koken ga Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Ingila".

Daga bisani kungiyar alkalan wasa ta PGMO ta fitar da wata sanarwa wadda ke cewa: "PGMO na sane da zarge-zargen kuma tana daukarsu da matukar muhimmanci.

"Mark zai bayar da cikakken hadin kai kuma yana marhabin da yunkurin tabbatar da gaskiya".

Dukkan jami'an da ke sa ido a kan wasa su hudu—alkalin wasa da mataimakansa biyu da kuma wani jami'in na hudu—kan sanya makirfo da lasifikar kunne wadanda kan ba su damar jin abin da ko wannensu ke fadi, ko da yake ba a nadar kalamansu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.