BBC navigation

Djabour ne Kociyan Congo-Brazzaville

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:12 GMT
congo brazzaville flag

tutar kasar Congo Brazzaville

Kasar Congo-Brazzaville ta nada Kamel Djabour a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafar kasar.

Djabour ya maye gurbin Jean-Guy Walleme ne, wanda harwayau shi ne yake horar da kulab din Auxerre, inda a nan ma Djabour ne yake masa mataimaki.

Shi dai Jean-Guy Walleme ya yi murabus daga horar da 'yan wasan kasar Congo-Brazzaville ne domin ya mai da hankali kan kulab din Auxerre, saboda a cewarsa ba za iya tauna taura biyu a baka ba.

Kasar Congo-Brazzaville dai ba ta samu shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi badi ba, amma ita ce gaba-gaba a rukuninta na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a shekara ta 2014 bayan wasu wasanni biyu da ta fafata.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.