BBC navigation

Ba na sha'awar aikin Blackburn, in ji Redknapp

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:36 GMT
harry redknapp

Harry Redknapp

Tsohon kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce ba shi da wani shiri na tattaunawa da kungiyar Blackburn a game da mukamin mai horad da 'yan wasanta bayan da ake rade-radin cewa yana shirin ganawa da klub din akan batun.

Blackburn wadda ta fice daga gasar Premier a kakar wasannin da ta gabata ta na neman wanda zai maye gurbin Steve Kean wanda ya bar aiki da kungiyar a watan Satumba.

''Ban gana da kowa daga Blackburn ba kuma ba ni da shirin yin hakan'' in ji Harry Redknapp

Kungiyar ta gana da tsohon dan wasan baya na Blackburn Henning Berg kuma maganar kocin Blackpool Ian Holloway har yanzu tana nan a gaban kungiyar.

Shi ma tsohon kocin Ingila Glenn Hoddle a na ganin klub din na duba yuwuwar tattaunawa da shi a kan mukamin.

Redknapp ne ake ganin zai sami mukamin kociyan Ingila lokacin da Fabio Capello ya ajiye mukamin a watan Fabrairu amma sai aka nada tsohon kocin Fulham Roy Hodgson, shi kuma Redknapp dan shekara 65 ya rasa mukaminsa na kociyan Tottenham a watan Yuni kuma tun a lokacin ba shi da aiki.

Blackburn ta kasance ba ta da kociya tun lokacin da Steve Kean ya ajiye aiki bayan watanni 18 a kungiyar lokacin da ta sami koma baya daga rukunin gasar Premier.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.