BBC navigation

Afrika ta kudu na zawarcin Surman

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:43 GMT
bafan bafana

Bafan Bafana

Kocin Afrika ta Kudu Gordon Igesund na fatan shawo kan dan wasan Norwich na tsakiya Andrew Surman domin ya bugawa kasar wasa a gasar cin Kofin kasashen Afrika ta 2013.

A baya dai Surman ya yi watsi da gayyatar da sauran kociyoyin Afrika ta kudun kamar su Carlos Alberto Parreira da Pitso Mosimane su ka yi masa na zuwa ya bugawa kasar wasa.

A wannan karon Igesund ya ce yana son ya sake jarrraba gayyatar dan wasan mai shekaru 26 wanda aka haifa a Johannesburg kafin daga baya ya koma Burtaniya tun yana dan yaro ko zai amsa kiran domin yana ganin zai taimakawa kungiyar wasan kasar sosai.

Dan wasan ya bugawa Ingila a matakin 'yan kasa da shekara 21 amma ya can-can- ta ya bugawa Afrika ta Kudu wasa bisa ka'idojin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA.

A watan da ya gabata Surman ya bayyana cewa shi kam yana son ya maida hankalinsa ne wajen neman gurbi a kungiyarsa ta Norwich.

Duk da wannan furuci na dan wasan, Igesund wanda zai je Ingila domin ganawa da shi yana ganin zai iya shawo kansa domin ya shigo kungiyar 'yan wasan ta Afrika ta Kudu, Bafana Bafana, musamman ma ganin cewa yanzu akwai gurbin da zai cike bayan da dan wasan Everton Steven Pienaar ya yi ritaya daga buga wasan kasa da kasa.

Kociyan na Afrika ta Kudu zai kuma yi amfani da damarsa ta zuwa Ingilan ya gana da sauran 'yan wasan kasar da ke Ingilan wadan da suka bayyana aniyarsu ta yin ritaya daga bugawa kasar wasa da su sake shawara domin fitar da kasar kunya ganin cewa a kasar tasu za ayi gasar.

A wannan makon ne kocin zai sanar da jerin 'yan wasansa na karshe da zasu buga gasar cin kofin Afrikan a karawar da za su yi ta sada zumunta da zakarun Afrika Zambia, kafin gasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.