BBC navigation

Henning Berg zai zama kocin Blackburn Rovers

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:35 GMT
Henning Berg

Henning Berg

Tsohon mai tsaron baya na kungiyar kwallon kafa ta Blackburn Rovers, Henning Berg, na daf da rattaba hannu a kan wani kwantiragi na shekaru uku don zama sabon kocin kungiyar.

Zuwan kocin mai shekaru arba'in da uku, wanda ke da kwarewar shekaru shida a kasarsa ta haihuwa, wato Norway, zai kawo karshen farautar da ake yi ta magajin Steve Kean.

Berg, wanda ake sa ran za a gabatar da shi ranar Alhamis, zai karbi ragamar kungiyar ce a daidai lokacin da take matsayi na biyar a kan teburin Gasar Premier.

A zamanin da ya ke kungiyar, ya buga mata wasanni dari uku; kuma yana buga mata wasa lokacin da ta yi nasarar lashe Gasar Premier a shekarar 1995.

Wata guda ke nan kungiyar ta Blackburn ba ta nada magajin Kean ba, wanda ya yi murabus ranar 28 ga watan Satumba bayan ya yi watanni ashirin da daya yana jagorancinta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.