BBC navigation

A yada abin da alkalan wasa ke cewa —Palios

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:24 GMT

Wani jami'i ya yi kira a rika yada tattaunawar da alkalan wasa ke yi da 'yan wasa

Wani tsohon babban jami'i a Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Ingila, wato FA, Mark Palios, ya yi kira da a rika yada abin da alkalan wasa ke cewa ta yadda 'yan kallo za su rika ji.

Kiran ya biyo bayan takaddamar da ta barke ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da alkalin wasa Mark Clattenburg.

Hukumar ta FA da ma 'yan sanda sun fara bincike a kan zargin da kungiyar ta Chelsea ta yi cewa Clattenburg ya furta kalaman da ba su dace ba, ciki har da na nuna wariyar launin fata, ga 'yan wasanta biyu.

"Ban ga dalilin da zai hana a rika nadar abubuwan da alkalan wasa ke cewa ba", inji Palios a wata hira da ya yi da BBC.

Ya kuma kara da cewa "Da an nadi kalaman da mun samu amsa a kan ko ikirarin kungiyar ta Chelsea na da tushe".

Palios ya yi amanna yada musayar kalaman da alkalin wasa ke yi da 'yan wasa kamar yadda ake yi a wasannin kwallon zari-ruga zai amfani yekuwar "mutunta Juna" da hukumar FA ke yi ta hanyar fitowa fili da irin kalaman batancin da jami'an wasa ke fama da su.

A wuraren manyan wasannin zari-ruga dai 'yan kallo na da damar sayen lasifikar kunne ta Ref Link don su rika jin irin tattaunawar da jami'an wasa ke yi da 'yan wasa; masu kallon talabijin ma kan ji tattaunawar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.