BBC navigation

Di Matteo ya ce 'yar manuniya ta nuna gaskiya.

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:11 GMT
chelsea da manchester united

Chelsea da Manchester United

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roberto Di Matteo, ya ce sakamakon wasan Cin Kofin kalubale na Capital one tsakanin kungiyarsa da Manchester United 'yar manuniya ce ta nuna.

Di Matteo ya ce nasarar da 'yan wasansa suka yi a kan Manchester United da ci biyar da hudu ta nuna karara cewa sakamakon wasansu na ranar Lahadin da ta gabata babu gaskiya.

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar ta Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester United da ci uku da biyu a gasar Premier.

Kocin kungiyar Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya kasa cewa komai game da wasan nasu na ranar Laraba.

Di Matteo dai ya fusata da alkalin wasan Mark Clattenburg bayan da alkalin ya kori Fernando Torres daga wasa.

Ana dai zargin Clattenburg da furta kalaman wariyar launin fata ga dan wasan tsakiya na Chelsea John Mikel Obi.

Sai dai a wannan wasa na cin kofin Capital One Di Matteo korafi daya ya yi a kan yadda alkalin wasan, Lee Mason, ya yi watsi da ikirarin Juan Mata cewa ya kamata a ba shi bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.